Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Emanuela Del Re yana cewa kungiyar ta EU tana shirin karawa kasar ta Mali takunkuman tattalin arziki a bangarenta idan ta ki gudanar da zabubbuka kamar yadda aka tsara.
Kafin haka dai sojojin masu juyin mulki a kasar ta Mali sun dage shirin mika mulki ga fararen hula a farkon wannan shekarar da muke ciki, zuwa wasu shekaru 4 masu zuwa. Kasar Mali wacce take fama da tashe-tashen hankula tun bayan juyin mulki na shekara ta 2012, ta ce ta dage lokacin zaben ne don matsalolin tsaron da kasar take fama da su.
Kasar Faransa tana da dubban sojojin a kasar Mali tun shekara ta 2013 da sunan yaki da yan ta'adda, amma tun lokacin 'yan ta'addan sai kara karfi suke.
342/