Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

18 Janairu 2022

13:58:15
1220233

​Burtaniya: Matsin Lamba Na Karuwa A Kan Johnson Da Ya Yi Murabus

Firayi Ministan Burtaniya na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga bangarorin siyasa a kasar da ke neman ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ana sa ran yan majalisu kama daga masu goyan bayan sa da masu adawa da manufofin gwamnatin sa za su kada kuri’ar yanke kauna, wanda hakan zai tilasta masa mika takardar murabis.

Hukumar bincike ta musaman da aka kafa na ci gaba da aikinta domin gano gaskiyar lamarin tun bayan da aka gano cewa Firaministan ya keta dokar kasar Birtaniya, tare da shirya liyafa a wani lokacin da bai dace ba, musaman lokacin da cutar Covid 19 ke barrazana ga rayuwar al’uma aka kuma hana shirya tarruruka, biki ko makamancin haka.

Wasu daga cikin ’yan jam’iyyarsa na fatan ganin ya sauka daga mukaminsa na Firaminsta, to amma kuma wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar tasa suna ganin za a iya fuskantar matsalar shirya wasu zabuka a cikin irin wannan yanayi da har yanzu ake fuskantar matsalr ta corona a kasar ta Burtaniya.

342/