Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Litinin

17 Janairu 2022

14:49:56
1219958

Sakon Ta'aziyyar Majalissar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Dangane Da Rasuwar “Sheikh Abdullahi Nasser”

Wannan Malami ya kasance daya daga cikin manya jigogi na majalissar majalissar Ahlul Baiti (as) ta duniya kuma a tsawon rayuwarsa mai albarka ta hanyar rubuta littafai da dama ya taka rawa mai dorewa wajen yada koyarwar Ahlul Baiti (AS). -Bait (a.s) da kuma ilmantar da dimbin jama'a a kasar Kenya da makwaftan kasashe.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, bayan rasuwar Hajj Sheikh “Abdullahi Nasser Juma”, mamba a majalisar malamai ta Ahlul-baiti (AS) ta duniya kuma Babban Malamin Shi'a dan asalin kasar "Kenya", majalisar malamai ta Ahlul-baiti (AS) ta duniya ta fitar da sakon ta'aziyya na rashin wannan babban malami.
Gundarin Rubutun Wannan Sakon Yazo Kamar Haka:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Daga Allah Muke Kuma Gare Shi Zamu Koma
Rasuwar Malam Haj Sheikh Abdullahi Nasser, daya daga cikin manya kuma jiga-jigan 'yan Shi'a wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen yaduwar Shi'a a kasar Kenya, ta haifar da bakin ciki da radadi sosai.
Wannan Malami ya kasance daya daga cikin manya jigogi na majalissar majalissar Ahlul Baiti (as) ta duniya kuma a tsawon rayuwarsa mai albarka ta hanyar rubuta littafai da dama ya taka rawa mai dorewa wajen yada koyarwar Ahlul Baiti (AS). -Bait (a.s) da kuma ilmantar da dimbin jama'a a kasar Kenya da makwaftan kasashe.
Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta duniya tana mika ta'aziyya ga iyalansa masu daraja da dukkan abokansa da masoyansa, musamman 'yan Shi'ar Khoja Isna Ashar da sauran masoya Ahlul-baiti (AS) tana mai basu hakuri, da jajantan masutana mai rokon Allah madaukakin sarki day a bashi madaukakiyar daraja kuma ya bawa iyalansa daya bari hakurin rashinsa.
Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya
Janairu 11, 2021
21 Day 1400

Yana da kyau a san cewa marigayi Sheikh Abdullahi Juma Nasser ya kasance daya daga cikin malaman addinin Musulunci masana wanda tun shekaru hamsin na karni na ashirin, an sanshi a matsayinsa na mai wa’azi kuma malami, ya bunkasa da koyar da ilimin addinin Musulunci, a lokaci guda kuma ya tsunduma cikin harkokin adabi da yada sakonni na musulunci da ayyukan siyasa.

Ya kasance mai fafutuka a yunkurin neman yancin kai na Kenya daga mamayar turawan mulkin mallaka na Birtaniya daga 1957 zuwa 1963, kuma a lokacin da yunkurin ya kawo karshe ya kasance memba na babban taron tsarin mulki na tarihi a Lancasterhouse na Landan, wanda aka kafa don samun 'yancin kai daga daular Burtaniya inda ya taka rawar gani.
Sheikh Abdullahi Nasser, wanda daya ne daga cikin manya-manyan malamai masu wa'azi da malaman Sunna, kuma daya daga cikin manya da shehunan wannan tawaga a kasar Kenya, an haife shi ne a shekara ta 1975. Inda bayan nana ya fahimci mazhaba ta Shi'a. A wata hira da aka yi da shi dangane da dalilin da ya sa ya karkata zuwa ga Shi’a, ya ce: “Na fahimci falalar Amirul Muminina Ali (as) kuma a hankali na ji cewa Ali bin Abi Talib (as) shi ne mafi girman musulmi bayan Manzon Allah SAWA. Bayan wani lokaci, Na ci karo da Littafin Al-Ghadir na Marigayi Allama Amini, da na karanta juzu'i na farko, sai na gane halaccin 'yan Shi'a, sai na tafi masallacin 'yan Shi'a, bayan haka na karanta wasu litattafai da dama, daga karshe na zama dan shi’a”.
Bayan Hajj Abdullahi Nasser ya koma Shi'a, ya taka muhimmiyar rawa wajen shiryar da mutane zuwa wanan mazhaba a kasar Kenya da sauran kasashen Afirka ta hanyar rubuta litattafai da kasidu a kan Shi'anci.
Ya kafa makarantar hauza ta Imam Ali (AS) a yankinsa, kuma a wannan makaranta an horar da daruruwan dalibai makwafta da masu hijira a manyan matakai na ilimi da addini, tare da yada koyarwar Musulunci da Shi'a a tsakanin jama'arsu.
Wannan fitaccen malamin da yake da dimbin ilimin tarihin Musulunci da ka'idojin akidar Shi'a, ya kuma gudanar da muhawara da dama da malaman Wahabiyawa a kasar Kenya tare da kare mazhabar Ahlul Baiti (AS) na tsawon rabin karni.
Marigayi Abdullahi Nasser ya rubuta litattafai da kasidu sama da 25 a cikin harshen Swahili game da Musulunci da Shi’a, wasu daga cikinsu an fassara su da buga su cikin Turanci da harshen Ruwanda. Daga cikin littafai masu daraja da ya rubuta akan aqidar Shi'a akwai kamar haka;
ـ الشیعة والقرآن
ــ الشیعة والحدیث
ــ الشیعة والصحابة
ــ الشیعة والتقیة
ــ الشیعة والإمامة
Littafin "Shi'a da Taqiyya" na daya daga cikin muhimman ayyukansa wanda ya rubuta a matsayin martani ga wani littafi da Moheb al-Din Khatib ya wallafa mai suna " خطوط کلی" a cikin harshen Larabci sannan kuma a karkashin sunan ya sanya wannan unwani " Tushen Mazhabar Shi'a " Harshen Swahili inda hakan Ya haifar da shakku a tsakanin musulmin yankin Afirkadangane da abunda ke cikin wannan littafi, Marigayi Abdullahi Nasser ya yi bayani a kan akidar Taqiyya ta mahangar Shi’a. Ya ce dangane da littafin: “Saboda shubuhohin da suka taso a kan lamarin takiyya a Afirka, na ga ya dace in shirya wannan littafi tare da gabatar da shi ga jama’a domin kawar da shubuhar da ta taso tun farko. Wanda naga Ya kamata a fadakar da jama’a game da lamarin takiyya”.

Sunayen babi hudu na littafin "Shi'a da Taqiyyah" su ne:
1. Menene taqiya?
2. Matsalolin ‘yan Shi’a a zamanin Banu Umayyah da Banul Abbas;
3. Takiyya a wajen Ahlus-Sunnah;
4. Taqiyya a mahangar Shi'a.
Sannan an ci gaba da rarraba jerin jawabai na Sheikh Abdullahi Nasser na kaset da na sauti da na bidiyo a tsakanin al'ummar musulmin kasar, musamman a yankin tekun Indiya. Wadannan jawabai sun kasance daya daga cikin abubuwan da suka zaburar da al'ummar Afirka wajen komawa ga mazhabar Ahlul Baiti (AS) da kuma kawar da su daga tsattsauran ra'ayi na takfiriyya.
A cikin wadannan shekaru Wahabiyawa da cibiyoyinsu sun yi masa ayyuka da daman a kalubalantarsa da kuma kokarin kawar da shi daga Shi'anci ta hanyar cin hanci da barazana, amma ba su yi nasara ba.
Marigayi Abdullahi Nasser ya kasance wakilin al'ummar Mombasa a majalisar dokokin kasar kuma ya kasance mai farin jini a wajen jama'a.
Har ila yau, ya kasance “memba na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) a wannan kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa; Yayin da ya halarci zamomi da tarurruka daban-daban na kasa da na shiyya, ya yi tasiri ga masana da malaman addinin Musulunci na kasashen gabashin Afirka.
Halin yanayi na dantako, mutunci, dattijankata, daidaitawa da yalwar ɗabi'a, sun sanya wannan masanin Allah mai bincike a duniya abin koyi ga malamai da matasa.
A cikin shekarunsa na karshe na rayuwarsa masu albarkarsa, ya yi tafsirin kur’ani mai tsarki da harshen Swahili, daga karshe bayan rayuwarsa mai cike da bincike da inganta koyarwar Saqaleen, ya rasu a ranar Litinin 20 ga Day, 1400 / 11 ga Disamba 2022
An binne gawarsa bayan muminai sun masa rakiya a makabartar Ganjuni da ke Mombasa.

Allah Ta’ala Yayi Masa Rahama Da Rahamarsa. Yasa Annabi Da Iyalansa Da Alkur’ani Su Ceceshi.
......................
Dan Jarida Na Kasa Da Kasa / Sayyid Muslim Jazayeri