Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Jummaʼa

14 Janairu 2022

20:13:27
1218988

Jami'an Tsaron Turkiyya Sun Kama Wasu 'Yan ISIS + Hotuna

Dakarun Turkiyya na yaki da ta'addanci sun cafke mutane da dama da ake zargi da alaka da kungiyar ta'addanci ta Da'esh a garuruwa daban-daban.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, dakarun da ke yaki da ta'addanci na kasar Turkiyya sun cafke mutane da dama da ake zargi da alaka da kungiyar ta'addanci ta Da'ish a garuruwa daban-daban.

An gudanar da wannan samame mai suna Panja 2 a daren jiya a Mersin, Adana, Shanli Orfa, Bursa, Konya da Ghazi Aintab tare da hadin gwiwar sojoji 2,200 da jirage masu saukar ungulu 7, inda aka kama mutane da dama da ake zargi da 'yan ISIS ne.

Kafafen yada labaran Turkiyya sun ce an kama wasu makudan kudade da daloli da kuma takardun aiki daga maboyar mutanen.

342/