Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

13 Janairu 2022

20:08:47
1218680

​Faransa: An Rusa Majalisar Musulmi Tare Da Maye Gurbinta Da Wata Cibiya

Gwamnatin kasar Faransa ta maye gurbin majalisar musulmin kasar Faransa da wata cibiya mai suna majalisar musulunci a kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, daukar wannan matakin na zuwa ne domin aiwatar da wani daftarin kudiri mai suna Charter of Islamic Principles a kasar Faransa, wanda wasu kungiyoyin addinin musulunci a kasar suke ganin barazana ce ga hakki da hadin kan musulmi.

Gwamnatin Faransa ta sanar da kafa wata cibiya mai suna "Majalisar Musulunci a Faransa" domin maye gurbin majalisar musulmin Faransa, wadda a cewar gwamnatin bayan shekaru 20 da kafuwarta ke fama da rikice-rikice na cikin gida.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya amince da shirin, kuma nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani taro mai suna Majalisar Musulunci tare da wakilan musulmi a kasar.

Shi ma shugaban majalisar musulmin kasar Faransa Mohammad Mousavi ya bayyana goyon bayansa ga kafa majalisar musulunci, yana mai cewa majalisar ba ta iya ci gaba da gudanar da ayyukanta, don haka ya kamata a rusa ta; Sai dai kawo yanzu ba a bayyana adadin kungiyoyin Musulunci nawa suke son shiga sabuwar cibiyar ba.

A watan Nuwamban da ya gabata ne gwamnatin Faransa ta sanar da kafa Majalisar limamai ta kasa (CNI) a kasar Faransa a wani bangare na yaki da abin da ta kira Musulunci mai tsatsauran ra'ayi, wanda wasu ke ganin ya gurgunta ayyukan Musulunci a Faransa.

342/