Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

6 Janairu 2022

15:55:07
1216279

​Kasashe 5 Sun Fara Aiki A Matsayin Zababbun Mambobin Kwamitin Sulhu Na MDD

Kasashen Albania, da Brazil, da Gabon, da Ghana da kuma hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun fara aiki a matsayin mambobin da ba na dindindin ba a kwamitin sulhu na MDD.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2022 ne, wa'adinsu na shekaru biyu ya fara aiki a hukumance.

Ranar Talata, ita ce ranar farko ta fara aiki na majalisar na 2022, bayan dawowa daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

An gudanar da bikin daga tuta domin fara gudanar da ayyukansu.

Wakilan dindindin na sabbin mambobin majalisar biyar sun yi takaitattun jawabai kafin su sanya tutocin kasashensu a wajen zauren majalisar.

Kasashen biyar sun maye gurbin kasashen Estonia, da Jamhuriyar Nijar, da Saint Vincent da Grenadines, daTunisia, da kasar Vietnam.

342/