Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA 24
Talata

28 Disamba 2021

17:25:43
1213383

Mahangar AlKur'ani Game Da Annabi Isa (A.S) A Cikin Sakon Twitter Na Kirsimeti Da Shugaban Cibiyar Musulunci Ta Burtaniya Ya Rubuta

Shugaban cibiyar muslunci ta kasar Britaniya, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter na Kirsimeti, yayin da yake ishara da matsayin Annabi Isa AS a cikin kur’ani mai tsarki, ya sanar da gudanar da taron mabiya addinai na duniya domin yin nazari kan wannan batu a wannan cibiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, shugaban cibiyar muslunci ta kasar Birtaniya a wani sako da ya fitar a shafinsa na twitter dangane da bukukuwan kirsimeti, yayin da yake ishara da matsayin Annabi Isa a cikin kur’ani mai tsarki, ya sanar da gudanar da bikin taron addinai don nazarin wannan batu a wannan cibiya.
Hujjatul Islam Wal Muslimin “Sayyid Hashim Mousavi” wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Ingila kuma shugaban cibiyar Musulunci ta wannan kasa, dangane da haihuwar Annabi Isa As a shafinsa na Twitter na kashin kansa, yayin da yake taya al’ummar kasar murna ya sanarda cewa: mabiyan wannan annabi mai girma domin girmama wannan munasaba za’a gudanar da taron addinai a wannan cibiya a shekara mai zuwa.

Ya Rubuta A Adreshi Mai Suna: @moosavi54

"Aminci ya tabbata ga Isa, kalmar Allah." Ina fatan da albarkacin wannan Kirsimeti mai albarka, dukkanin bil'adama za su samu damar kubuta tare da kawar da mummunar cutar ta Corona da wuri-wuri. Sakamakon wasu bincike ya nuna cewa a cikin Alkur’ani mai girma an anbaci tare da girmama Annabi Isa (AS) sama da sauran littattafan addini masu daraja. Domin ci gaba da binciko wannan batu, za’a gabatr da taron kimiyya tare da halartar masana kiristoci da musulmi da yahudawa a cibiyar Musulunci ta Ingila. "In Allah ya yarda, idan muka yi nasara, za mu yi kokarin gudanar da wannan taro a shekara mai zuwa, a a lokacin haihuwar Sayyidana Isa As".

342/