Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

28 Disamba 2021

17:16:53
1213371

Sojojin kasar Turkiya Sun Kaddamar Da Hare-hare A Arewacin Kasar Iraki

Majiyar labaran kasar Iraki sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Turkiya sun kai hari a kauyen Batifa da ke gabashin Zakho a lardin Dukho dake yankin kurdawa kuma yayi sanadiyar jikkatar wata mace guda daya, haka zalika an kai wani harin a Arewacin Arbil dake yankin na kurdawa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Fadar shugaban kasar iraki ta yi Tir da harin da sojojin turkiya suka kai , tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin kasar da kuma take dokokin kasa da kasa, da zai iya kawo cikas a kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasahen dake makwabtaka da juna.

Wannan yana zuwa ne bayan da aka harba wasu makaman roka a sansanin sojojin kasar turkiya a lardin Nainawa dake Arewacin kasar iraki. Sai dai babu wani rahoto game da samun asarar rai a wajen , yankin Ba’ashika yana daya daga cikin yankin dake arewacin kasar Iraki inda sojojin turkiya suka kafa sansaninsu.

342/