Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

27 Disamba 2021

14:29:14
1213010

MDD Ta Yi Tir Da Kisan Da Aka yi wa Fararen Hula A Myanmar

Shugaban hukumar kula da kare hakkin dan Adam na Majalisar dinkin duniya Martin Grifffiths a cikin wani bayani day a fitar ya nuna cewa an kashe fararen hula akalla guda 35 da suka hada da mata da yara tare da kona gawarsu, a kasar Mayammar kana ya bukaci a gudanar da bincike kan kisan gillan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace ya kadu sosai lokacin da yaga hoton abin daya faru a da aka yada a kafafen sadarwa na zamani inda aka nuna yadda ake kona gawarwakin mutane a cikin manyan motoci, a kan babbar hanya dake jihar kayah kasar ta mayammar,

Yace akwai wasu ma’aikatan kungiyar agaji ta save the children suka yi bata dabo, bayan daka kai musu hari akan motocin kuma aka konasu kurmus.

Daga karshe ya bukaci gwamnatin kasar da ta gaggaunata kafa kwamiti domin gudanar da binciken kwakwaf kan sanadiyar afkuwar lamarin da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kutu domin su girbi abin da suka shuka.

342/