Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

26 Disamba 2021

18:11:32
1212713

​Putin Da Al’Sisi Sun Tattauna Game Da Batun Libiya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Masar, Abdel fatah Al-sisi, sun tattauna ta wayar tarho game da halin da ake ciki a kasar |Libiya.

Shugabannin biyu sun amince karfafa alaka a wani mataki na shayo kan rikicin Libiya.

Sun amince yakar ‘yan ta’adda, da kuma kawo karshen masu dauke da makamai da kuma ganin bayan sanya baki a cikin harkokin cikin gidan Libiya kamar yadda fadar shugaban Masar ta sanar.

Shugaban Masar Al’Sisi, ya fadawa twakwaransa na Rasha, anniyar kasarsa na taimakawa ‘yan Libiya, wajen zaben shugabaninsu da wakilansu cikin lumana.

A daya bangaren kuma shugaban Masar ya jadadda aniyarsa kasarsa ta karfafa alaka da Rasha ta dukkan bangarori.

Shi kuwa Putin, ya ce kasarsa za ta maida hankali wajen karfafa alaka ta ci gaba tsakanin kasashen biyu.

342/