Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Akalla mutum daya cikin hudu ne ke fuskantar barazanar yunwa a Somaliya a sabili da fari da kasar ke fuskanta a cewar Majalisar Dinkin Duniya a wani rahoton gargadin da ta fitar.
Wannan dai na zuwa ne bayan karancin ruwan saman da kasar ta fuskanta na kusan damina hudu a jere.
A cewar rahoton matsalar za ta yi kamarin da za ta kai ga barin kusan mutum miliyan 5 ga bukatar agajin gagawa na abinci.
Sama da shekaru 30 Somaliyar bata taba fuskantar irin wannan hali na fari da ta shiga ba.
A watan da ya gabata mahukuntan Somaliya suka ayyana wannan matsala ta fari a matsayin abun damuwa dake bukatar tallafin gaggawa.
342/