Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A ranar Juma'a ne cikin jawabin da ya yi a jajibirin bikin cika shekara 63 da kasar ta zama Jamhuriya, Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar, ya yi kira ga faransa da ta gudanar da bincike a kan mutuwar masu zanga zangar, lokacin da ayarin dakarunta ke kan hanyarsu ta zuwa Mali.
Ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta ce sojojin kasar sun yi iya kokarin ganin sun yi abin da ya dace a lokacin yamutsin.
Ministar ta kuma ce ana ci gaba da tattaunawa a kan batun da mahukuntan Jamhuriyar Nijar.
342/