Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Binciken yana zuwa ne bayan shugaban kasar Niger mohammad Bazoum ya bukaci a gudanar da bincike kan ayarin sojojin Faransa dake hanyarsu ta zuwa kasar mali da ya haddasa zanga-zanga da ta jawo asarar rayuka.
Akalla mutane 2 ne suka mutu wasu guda 18 kuma suka jikkata bayan da tawagar sojojin Faransa ta budewa huta domin tarwatsa masu zanga-zanga da suka tsare musu hanya a yammacin kasar Niger.
Ana ta bangaren kakakin sojojin kasar Faransa Pascal Lanni ya fadi cewa: “babu wani sojojin Faransa daya jikkata sakamakon taho mu gamar, sai dai wasu fararen hula guda biyu sun jikkata bayan da aka jefesu da duwatsu.
Daga karshe ta bayyana cewa suna ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Niger domin gano hakikanin abin da ya faru kafin da lokaci da kuma bayan afkuwar hargitsin.
342/