Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

20 Disamba 2021

16:20:16
1210511

Shugaban Turkiya Ya Bayyana Rashin Wakilcin Afrika A Kwamitin Tsaro A Matsayin Rashin Adalci

Rajab Dayyib Ardigon shugaban kasar Turkiya ya bayyana hakan ne a wajen taro tsakanin turkiya da nahiyar Afrika na yini biyu da ka kammala a jiya Asabar , inda ya ce taron yana iya zama wata damace ta kara fadada huldar kasuwancin ta sayar da jiragen sama mara matuki,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Yana mai cewa akwai rashin Adalci sosai inda Nahiyar Afrika dake da yawan mutane miliyan 1.3 amma ba shi da wakilci ko daya a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya.,

Taron wata dama ta kasuwancin, kuma Turkiya za ta kara fadada huldarta ta fuskacin tsaro da kasashen Afrika kuma tana da tsari mai kyau na yaki da sayar da jirage mara matuki.

Kasar Turkiya na ci gaba da kara sanya sawunta sosai a nahiyar Afrika inda a gomiya 2 da suka gabata ta bude wasu ofisoshin jakadanci guda 30, Kuma ta kafa sansanin soji a kasashen Sumaliya, Moroko da kuma Tunusiya, wanda ko a watan Satumba ma an kai jiragen sama mara matuki na Turkiya zuwa yankunan.

342/