Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

19 Disamba 2021

13:20:06
1210131

​An Kammala Taron Afrika Da Turkiyya

An kammala taron Afrika karo na uku da ya gudana a ranar Asabar, inda wakilai daga kasashen Afrika kimanin arba’in suka halarci taron.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Sanarwar bayan taron ta ce an sanyan hannu kan manyan ayyuka da za’a cimma a cikn shekaru masu zuwa da suka hada da karfafa zaman lafiya da tsaro, gine gine, kasuwanci, ilimi da dai saurensu.

Za’a aiwatar da ayyukan a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2026 inda Turkiyya zata karfafa kasuwanci da Afrika.

Shugaban kwamitin tsaro da zaman lafiya na Afrika, Musa Faki, ya bayyana a yayin taron cewa sun kwashe tsawon shekaru goma suna neman tallafi daga kwamitin tsaro amma basu samu wani abu daga tallafin MDD ba.

Shi kuwa shugaba kungiyar tarayyar Afrika na wannan karo kana shugaban RDC, Félix Tshisekedi, bukatar zuba jari ya yi.

342/