Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Faransa da Hollande na daga cikin kasashen turan da suka sanar da daukar irin wannan matakin.
Firanministan Faransa Jean Castex ya ce nau'in cutar korona na Omicron na bazuwa a Turai tamkar wutar daji, abin da ya sa aka hana bukukuwan ranar sabuwar Shekara a birnin Paris.
Ya ce akwai alamun zai zama nau'in cutar mafi bazuwa a Faransa.
Haka kuma kasashen turai da dama sun tsauraran matakan shiga Burtaniya, inda Omicron ya fi yaduwa a duka nahiyar.
A Ireland ma, hukumomi sun ce za a dinga rufe gidajen cin abinci daga karfe takwas na dare, za kuma a rage adadin mutanen da ke shiga kallon wasanni.
342/