Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

19 Disamba 2021

13:16:41
1210128

​EU: A Yanzun Mun Fahinci Juna Dangane Da Dagewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki

Mataimakin jami’i mai kula da al-amuran harkokin wajen ta tarayyar Turai Enrique Mora ya bayyana cewa a halin yanzu kungiyar ta sami matsaya guda da kasar Iran a shawarar da ta gabatar na dauke mata takunkuman tattalin arziki wanda Amurka ta dora mata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mora yana fadar haka a shafinsa na twitter a safiyar yau Asabar, bayan an kammala zagaye na 7 na tattaunawa tsakanin Iran da kasashen na Turai dangane da dauke mata takunkuman tattalin arzikin wadanda Amurka ta dora mata.

Jami’in na tarayyar Turai ya kammala da cewa mai yuwa taro na gaba, wato na 8 zai zama na karshe a kan wannan batun.

Kafin haka dai shugaban tawagar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran a tattaunawar Ali Baghiri ya bayyana cewa kasashe 3 na tarai wadanda aka fi sani da E3 wato Faransa Burtania da kuma Jamus, wadanda kuma suka sanya hannu a yarjejeniyar JCPOA na shirin nukliyar kasar Iran a shekara ta 2015 sun amince da shawarar wacce Iran ta gabatar kunshe da hujjuji kwarrar ta yadda za'a dage mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.

Baghiri yace a halin yanzu makomar tattaunawar tana hannin kasashen na Turai, shawarar da suka yanke ita ce zai fayyace matsayin da Iran zata dauka nan gaba.

342/