Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

16 Disamba 2021

13:25:58
1209235

​WHO: Sabon Nau’in Cutar Corona Na Omicron Na Yaɗuwa Cikin Sauri A Duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa sabon nau'in cutar korona na Omicron yana yaduwa cikin sauri a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A cikin rahoton da hukumar ta fitar, ya zuwa yanzu an samu wadanda suka kamu da sabon nau'in cutar a kasashe 77 a duniya. Sai dai a taron manema labarai, shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ta yiwu cutar ta shiga wasu karin kasashen a nan gaba, inda ya ce babban abin damuwa shi ne, yadda ba a yi wani tanadi ban a dakile yaduwar cutar.

Y a ce: "Tabbas kawo yanzu mun koyi darasi kan abin da ya faru a baya game da yadda muka dauki barkewar korona abin wasa, mun gane cewa lamarin ya wuce tunaninmu.

Ko da Omicron ba ta haddasa matsananciyar rashin lafiya ba, yawan masu kamuwa da cutar zai sa fannin kiwon lafiya ya jigata matuka, a cewarsa.

An fara ganin nau'in Omicron a kasar Afirka ta Kudu a watan Nuwamban day a gabata, tun daga lokacin ne kuma ake ta gano masu kamuwa da sabon nau'in cutar.

A baya-bayan nan shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu ya kamu da cutar, ana kuma yi masa magani, duk da cewa babu alamun cutar a zahiri tare da shi.

Wasu kasashe sun sanya wa Afirka ta Kudu da kasashe makwbta haramcin shiga kasarsu, bayan bullar nau'in na Omicron, amma hakan bai hana cutar yaduwa a kasashen duniya ba, musamman ma kasashen turai, inda a halin yanzu nan tafi zama kamar wutar daji.

342/