Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A rahoton da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar, dangane da burin sake fasalta rundunar sojin Faransar a yankin Sahel a 2022 mai shirin kamawa, Babban Kwamandan Rundunar ta Bakhan Janar Laurent Michon ya bayyana cewa, suna kan mataki na karshe ne, abin nufi shi ne na janye sojojin da ke yankin arewacin kasar Mali a garuruwan Tombouctou, Kidal, da Tessalit), a wasu lokutan aikin na tafiya ne tare da sa hannun mahukuntan Mali, da kuma na rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Mali Minusma, sai kuma aminai na rundunar hadin guiwar kasashe.
Janye dakarun da ke tafiya mataki-mataki na tafiya dai dai kamar yadda aka tsara.
A wannan fage da aka raba tsakanin rundunar Faransa da ta dakarun Majalisar Dinkin Duniya Minusma, alakar za ta ci gaba da tafiya ne ba canji domin dakarun Mali ne za su canji sojin na Faransa a cewar kwamandan na dakarn Faransa.
Zango na biyu na janye dakarun kuma, zai fara a cikin watanni 3 masu zuwa.
342/