Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

14 Disamba 2021

18:54:44
1208649

Kungiyar EU, Amurka Da Birtaniya Sun Yi Barazanar Kakabawa Kasar Rasha Takunkumai

Ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun hadu a birnin Brussel ajiya litinin sun zargi Mosko da tattara dakaru a kusa da iyakar kasar Ukrain a shirin da take yin a yi wu war kai mata hari.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Tuni dai kasar Rasha ta musanta zargin shirin kai hari kasar Ukrani, kana ta zarfin Kiev dake samun goyon bayan kasashen yamma da daukar mataken tsokana, wasu masharhanta sun bayyana goyon bayan ido rufe da kasashen turai ke bawa Ukrain a matsayin abin kunya.

Takunkuman da kasashen Turai din ke son kakabawa kasar Rasha sun hada da hana jami’an gwamnati yin tafiye –tafiye da kuma rike kadarorinta a kasashen waje da hakan zai shafi tsarin bakunan kasar, kuma me yi wuwa ne su dakatar da yarjejeniyar shimfida bututun iskar gasa da aka cimma tsakanin rasha da Jamus, sai dai Rasha ta yi gargadi game da sake duk wata tsokana ,

Sai dai masana sun yi amanna cewa kasashen turai da Rasha manyan abokan kasuwanci ne musamman a bangaren makamashi.

342/