Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

12 Disamba 2021

10:53:34
1207791

Iraki: An Kawo karshen Ayyukan Yaki Na Sojin Amurka A Cikin Kasar

Shugaban majalisar tsaron kasa a Iraki ya sanar da cewa, an kawo karshen yakin da sojojin kawancen Amurka suke yi a Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Kassim al-Araji, shugaban majalisar tsaron kasa a Iraki ya sanar a hukumance cewa an kawo karshen yakin da dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta a Iraki.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a yau Alhamis, a zagaye na karshe na tattaunawa da jami'an kawancen kasashen duniya da aka fara a bara, a hukumance mun sanar da kawo karshen aikin soji da kuma ficewarsu daga Iraki.

Ya kara da cewa: Daga yanzu za a ci gaba da hulda da dakarun hadin gwiwa a fagen ba da shawarwari, horarwa da karfafa gwiwa.

A ranar 5 ga Janairu 2020, kwanaki biyu bayan kisan Qassem Soleimani da al-Mohandes, majalisar dokokin Iraki, ta amince da korar sojojin Amurka tare da ayyana ta a matsayin doka.

Bangarori daban-daban na al'ummar kasar Iraki suna ci gaba da yin kira ga gwamnatin kasar da ta tabbatar da cewa ta aiwatar da wannan kudiri na majalisar dokokin kasar, wanda ya bukaci ftar da sojojin Amurka daga kasarsu.

342/