Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

9 Disamba 2021

16:40:13
1206928

Duniya Na Fatan Yin AIki Tare Da Sabon Shugaban Gwamnatin Jamus

Kasashen duniya na ci gaba da aike wa da sakon taya murna ga sabon shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, tare da fatan yin aiki tare da shi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen da kuma shugaban majalisar EU Charles Michel sun aika da sakon murnarsu ga sabon shugaban gwammnatin na Jamus tare da alkawarin yin aiki tare.

Shi ma a nashi sakon, shugaban kasar Chaina, Xi Jinping ya taya Scholz murna, ya na mai cewa Beijing zata yi aiki da shi don inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a sabon mataki.

Haka kasar Rasha, ta yi masa murna tare da fatan inganda alakar dake tsakanin kasashen biyu.

A jiye ne Olaf Scholz mai shekaru 63 ya sha rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar Jamus ta Bundestag.

Ya zama shugaban gwamnati na tara bayan karshen yakin duniya na biyu, Inda ya maye gurbin Angela Merkel da ta kwashe shekaru 16 kan karagar mulki.

342/