Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Talata

7 Disamba 2021

14:48:49
1206247

Jami’an tsaro A Turkiya Sun Dakile Yunkurin Kashe shugaban kasar Dayyib Rajab Erdogan

A wani rahoto da kafafen watsa labaran kasar Turkiya suna watsa ya nuna cewa jami’an yan sanda sun gano wani abin fashewa a wurin da shugaban kasar yake jawabi a kudancin kasar Turkiya, sai dai tuni suka kwance shi tare da kawar da shi daga wajen.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Tuni kwararrun masu binciken kwakwaf suka duba Naurar fashewar da motar yan sanda don gano hotuna da yatsun hannu, domin gano wadaanda ke da hannu wajen yun kurin kisan.

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da kasar take cikin matsananincin yanayin tarbarbarewar Tattalin arziki sakamakon faduwar darajar kudin kasar wato Lira akan dalar Amurka,

Darajar Takardar kudin ta Lira ta fadi da kash 40% akan dalar Amurka a bara, wanan yasa Erdogan ya canza gwamnan bankin kasar har sau 3 a cikin shekaru biyu.

342/