Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

6 Disamba 2021

14:38:31
1205869

Burtaniya Ta Kara Tsananta Binciken Lafiyar Masu Shigowa Kasar Saboda Omicron

Kasar Burtaniya ta bukaci dukkan matafiya da suke shigowa kasar su tabbatar da cewa suna da shaidar gwajin lafiya ta cutar Covid 19 kafin su shiga jirgi zuwa kasar, sannan duk ‘yan Najeriya wadanda suka shigo kasar ko suna da gwajin cutar lafiya na cutar ta Covid 19 dole sai sun kebe kansu na makonni biyu kafin su shiga gari.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ministan kiwon lafiya na kasar Burtaniya Sajid Javid yana fadar haka a jiya Asabar.

Kafin haka dai firai ministan kasar ta Burtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki tsauraran matakai kan matafiya masu shigowa kasar ne don tabbatar cewa cutar Covid 19 nau’in Omicron wacce ake bincike a kanta a halin yanzu bata yadu a kasar ba.

Har’ila yau cibiyar kula da harkokin lafiya ta kasar ta bada sanarwan cewa, ya zuwa yanzu an sami mutane 160 na wadanda suka kamu da sabuwar Covid 19 nau’in na Omicron a kasar ta Burtania.

342/