Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

5 Disamba 2021

16:26:37
1205509

​Rasha Ta Bukaci Isra’ila Da Ta Shiga Tattaunawar Kawar Da Makaman Nukiliya

Wakilin Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna ya yi kira ga gwamnatin Isra’ila da ta shiga tattaunawa kan kawar da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi a yankin gabas ta tsakiya

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Wakilin Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya yi kira ga gwamnatin sahyoniyawan da ta shiga cikin shawarwari na kawar da makaman nukiliya da makaman kare dangi a yankin gabas ta tsakiya

A jiya ne aka kammala zama na biyu na taron koli na kokarin ganin an kawar da makaman nukiliya a fadin yankin gabas ta tsakiya, amma Amurka da gwamnatin Isra'ila ba su shiga taron ba.

Mikhail Ulyanov ya ce taron na da matukar muhimmanci ga kasar Rasha domin shi ne mataki na farko kuma na hakika na hada kai don samar da yankin da babu makamin nukiliya a yankin gabas ta tsakiya, Wannan aiki zai kasance mai tsawo da wahala.

A halin yanzu dai Isra’ila ce kawai take mallakar makaman nukiliya a yankin gabas ta tsakiya, duk kuwa da cewa manyan kasashen duniya ba su taba mayar da hankali kan makaman nata ba, kamar yadda kuma hukumar makamashin nukiliya ta duniya ma ba ta taba daukar matakin matsin lamba a kanta tare da sanya ido a kan shirin nata ba.

342/