Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

3 Disamba 2021

16:10:09
1204765

Ziyarar Macron A Yankin Golf, Na Da Nasaba Da Cinikin Makamai

Shugaban kasar faransa Emanuel Macron zai fara wata ziyarar a kasashen Larabawan yankin Golf a wannan Juma’ar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ziyarar za ta fara kai shi a Hadadiyyar Daular Larabawa, kafin daga bisani ya isa Qatar, sai kuma Saudiyya inda zai karkare ran gadin nasa.

A hadaddiyar Daular Larabawa Macron zai sanya hannu kan yarjeniyoyin da dama da kasar.

A wani bayani da mujalar Challenges, ta fitar a watan Nuwamba ta ce akwai yiwuwar faransa ta kula yarjejeniyar ciniki ta sayar wa da Hadaddiyar Daular Larabawar jiragen yaki kirar rafale kimanin talatin zuwa sitin.

Faransa wadda ita ce ta uku wajen sayar da makamai ga kasashen duniya, na kallon Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin aminanta da ke yi mata biyayya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kafin hakan dai kungiyoyin Kare Hakkin dan adam sun shafe tsawon lokaci suna zargin Faransa da hannu wajen aikata laifukan yaki a Yemen.

Wasu bayanan sirri da aka bankado a cen baya sun nuna cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudi Arabiya na amfani da makaman da suka saya daga Faransa wajen kai hare-hare a Yemen.

342/