Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Disamba 2021

14:16:31
1204178

​Rawar Da Faransa Ke Takawa Da Tasirinta A Kan Wasu Kasashen Nahiyar Afirka

Faransa ta aike da dakaru sama da 5,000 zuwa yankin Sahel na Afirka, bisa ikirarin taimakawa kasashen yankin wajen yakar ta'addanci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Yankin Sahel yana kudu da hamadar Sahara kuma ya taso daga Tekun Atlantika a Yamma da kuma Bahar Maliya a gabas.

Yankin da ya kai girman Turai kuma mai arzikin albarkatun kasa kamar su man fetur, zinare, lu'u-lu'u, uranium, cobalt da sauransu, wanda ya hada kasashen Mauritania, Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi.

A cikin shekaru goma da suka wuce, kasancewar sojojin Faransa a yankin Sahel ya zo daidai da karuwar matsaloli na kabilanci a yankin, da kuma ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda kamar ISIS, Al-Qaeda da Boko Haram.

Firaministan kasar Mali Choguel Kokalla Maiga ya fada a cikin watan Oktoba cewa: yana da shaidar cewa sojojin Faransa na tallafawa da kuma horar da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar da ke yammacin Afirka.

A makon da ya gabata, dubunnan masu zanga-zanga a Burkina Faso sun tare ayarin motocin sojojin Faransa da ke wucewa cikin kasar. Masu zanga-zangar sun yi imanin cewa sojojin Faransa na jigilar manyan makamai da alburusai zuwa ga 'yan ta'addar.

Sojojin Faransa sun bude wuta tare da jikkata wasu da dama. Ayarin motocin na Faransa da suka isa nahiyar Afirka a Ivory Coast a farkon wannan wata, sun tsallaka Burkina Faso inda a ranar Juma'a suka shiga jamhuriyar Nijar kan hanyarsu ta zuwa tsakiyar kasar Mali.

Tsohon shugaban Faransa François Mitterrand ya taɓa cewa idan ba da Afirka ba, Faransa ba za ta sami gurbi ba a ƙarni na 21. Wani tsohon shugaban Faransa, Jacques Chirac, ya bayyana irin wadannan kalamai a shekara ta 2008, yana mai cewa idan ba don Afirka ba, Faransa za ta koma matsayi na uku a duniya.

Shugaban Faransa na yanzu ya kuma jaddada a kwanakin baya cewa Faransa za ta ci gaba da zama a Mali, Burkina Faso, Chadi, Mauritania da Nijar don taimakawa wajen yaki da ta'addanci.

Faransa ta yi amfani da kungiyoyin 'yan ta'adda don tabbatar da kasancewarta na tsawon lokaci da wawashe albarkatun kasa na Afirka.

Wani bayyani na hakikanin abubuwan da ke faruwa a Afirka ya nuna dalilin da ya sa Faransa ta kaddamar da wasan "yan sanda da 'yan fashi" a nahiyar.

Karfe na Hasumiyar Eiffel, kamar karfen da ake amfani da shi a masana'antun kera motoci na Faransa, ana samar da su ne daga Aljeriya da Mauritania.

Uranium da Faransa ke bukata domin samar da makamashin nukiliya ya fito ne daga ma'adinan Nijar da Chadi.

Faransa na shigo da mai daga Aljeriya da Gabon. Cocoa ta take shigowa da shi daga Ivory Coast ne ake yin cakulat da a Faransa. Masana'antun kayan ado na Faransa na amfani da zinare da ake shigo da su daga Mali da lu'u-lu'u daga Guinea.

Ana amfani da cobalt na Kongo wajen kera kayan sadawa a Faransa. Sannan kuma turaren Faransa daga furannin tsibirin Comoros ake yi shi, da kuma zaren ulu na Faransa daga Senegal ake shigo da shi. Hakanan ana amfani da itacen Kongo don ayyukan katako a Faransa.

Wadannan bayanai sun isa su zama dalili da ke tabbatar da cewa Faransa ta dogara ne da Afirka, kuma ba don Afirka ba to da babu Faransa a matsayin kasa mai karfin fada a ji yanzu a duniya.

342/