Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Disamba 2021

14:11:11
1204172

​Faransa: Mutane Kimani 47,000 Suka Kamu Da Cutar Covid 19 A Jiya Talata

Ministan kiwon lafiya na kasar Faransa ya bada sanarwan cewa mutanen kasar kimani dubu 47 ne suka kamu da cutar Covid 19 a kasar a ranar Talata kadai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : na kasar Iran ya nakalto Olivier Veran ya na fadawa ‘yan majalisar dokokin kasar ta Faransa kan cewa idan wannan yanayin ya ci gaba kasar Faransa zata shiga matsaloli masu yawa fiye da na baya kan abinda ya shafi yaduwar cutar ta Covid 19.

Ministan ya ya ce an yiwa kasha 75% na mutanen kasar alluran riga kafin cutar har guda biyu, wanda kuma adadinsu ya kai miliyon 50,876,798, ya kara da cewa akwai bukatar sauran mutane miliyo 6,000,000 wadanda basu yi alluran bas u gaggauta yinta.

Banda haka ministan ya bayyana cewa jami’an kiwon lafiya na sanya ido a kan mutane 8 wadanda ake zaton sun kamu da nau’in cutar ta Covid19 Omicron sabuwa wacce ta bulla a kasar Afirka ta kudu.

342/