Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Disamba 2021

14:10:22
1204171

WHO, Ta Bukaci Hadin Kan Duniya Kan Sabon Nau’in Korona Na Omicron

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bukaci kasashen duniya su hada kai wajen daukar matakan tunkarar sabon nau’in annobar korona na Omicron.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Yayin wani taron bada labara ga kasashe mambobin hukumar, a Geneva, Mista Ghebreyesus, ya ce a tafi tare a tsaire tare shi ne kawai mafita a daidai wannan lokaci.

Ina sane da damuwar da ko wacce kasa take da shi ga al’ummarta kan sabon nau’in da ba mu kai ga gane shi ba sosai, amma inda da muwa game da irin matakan da wasu kasashe suke dauka cikin gaggawa ba wata hujja, wanda kuma hakan zai kara haifar da rashin adalci.

Shugaban hukumar ta WHO, ya kuma jinjinawa kasashen Afrika ta kudu da kuma Boswana kan binciko sabon nau’in tare da sanar da duniya cikin gaggawa, saidai ya nuna damuwa akan yadda aka kyamaci kasashen bayan sun yi abinda ya dace.

Sabon nau’in koronar wanda aka gano a makon da ya gabata, a kudancin Afrika, kawo yanzu ta bazu zuwa dukkan nahiyoyin duniya.

342/