Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

27 Nuwamba 2021

12:01:17
1202769

WHO: Jami’an Kiwon Lafiya ¼ Ne Kawai Suka Yi Cikekken Alluran Riga Kafin Covid 19 A Afirka

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bada sanarwan cewa binciken da ta gudanar a nahiyar Afirka ya tabbatar da cewa kashi ¼ ko kuma kashi 27% ne na jami’an kiwon lafiya a nahiyar ne suka yi cikekken alluran riga kafin cutar Coved 19.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto daraktan hukumar ta WHO a nahiyar Dr Matshidiso Moeti ne ta bayyana haka a wata hiri da ta yi da manema labarai a ranar Alhamis. Ya kuma kara da cewa a cikin kasashen 25 da ta bi bincike a cikinsu ta gano cewa daga watan Maris na shekara ta 2021 ya zuwa lokacin bada labarin jami’an kiwon lafiya miliyon 1.3 ne kacal suka yi alluran riga kafin cutar, inda a cikinsu kasa guda ce ta yiwa kasha 90% na jami’an kiwon lafiyanta cikekken alluran.

Moeti ya kara da cewa kasashe 9 ne suka yiwa kashi 40% na jami’an kiwon lafiyarsu cikekken alluran. Da wannan kuma muna iya cewa mafi yawan jami’an kiwon lafiya a nahiyar suna cikin hatsarin kamuwa da cutar don basu yi cikekken rigakafinsa ba.

Daga karshe Moeti ya kammala da cewa idan ba’a yiwa likitov da jami’an jinya cikekken alluran ba akwai barazanar cutar zata babbar illa nan gaba.

342/