Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

22 Nuwamba 2021

13:10:35
1201134

WHO: Ta Gargadi Kasashen Turai Da Yiyuwar Mutuwar Mutane Dubu 500 Saboda Yaduwar Cutar Coved 19

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta gargadi kasashen turai kan su dauki makatan da suka dace don rage yaduwar cutar Covid 19 a kasashen yankin, saboda idan halin da ake ciki ya ci gaba mai yuwa mutane dubu 500 su mutu sanadiyyar cutar, nan da karshen watan Maris na shekara ta 2022.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Hans Kluge wani masani na hukumar lafiya ta duniya ya na fadar haka, ya kuma nuna damuwarsa da yadda cutar take kara yaduwa a kasashen na Turai, sannan ya bukaci gwamnatocin kasashen nahiyar, musamman na kasashen Jamus da Austria da su dauki matakan tilastawa mutanensu sanya takunkuman rufe baki, wanda zai iya yin tasiri wajen rage saurin yaduwar cutar a kasashen nasu.

KlugeCalugeh ya kara da cewa, zuwan fasalin sanyi, da kuma samuwar nau’in cutar ta Delta ya kara saurin yaduwarta a cikin wadannan kasashe, don haka dole ne a dauki matakan kiwon lafiya masu tsanani sannan kara sauri wajen yiwa mutane alluran riga kafin cutar saboda dakile ta.

342/