Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

21 Nuwamba 2021

16:01:38
1200833

Nijar Za Ta Sayi Jiragen Yaki Marar Matuki Kirar TB2 Na Turkiyya

Jamhuriyar Nijar za ta sayi kayaykin yaki na Turkiyya, da suka hada da jirgage yaki marar matuki kirar TB2, da motoci masu sulke.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan bayanin ya fito bayan wata tattaunawa ta wayar tarho a makon nan da ta wakana tsakanin shugaba Recep Tayyib Erdogan da takwaransa na Nijar Mohamed Bazoum.

Wata sanarwa da ofishin hulda tsakanin kasashen biyu ya fitar, ta ce bangarorin sun kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi yankunan.

A cewar labarin Shugaba Erdogan, ya bayyana cewa sayan jiragen marar matuka na Turkiyya zai taimakawa Nijar gayen wajen karfafa sojojinta da kuma yaki da ta’addanci.

Turkiyya dai ta yi kaurin suna wajen sayar da irin wadanan jiragen yakin marar matuki, inda ko a watan da ya gabata kamfanin kera jiragen na Baykar ya yaba da cimma yarjeniyoyi da kasashe 13 da suka hada da Qatar, Ukraine, Azerbaijan, Morocco da kuma Poland.

342/