Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

20 Nuwamba 2021

14:55:45
1200478

Blinken Ya Isa Senegal, Inda Zai Kammala Ziyararsa A Afrika

Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya isa Dakar babban birnin kasar Senegal, inda zai kammala ziyarar da ya soma a Afrika.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Yayin ziyarar tasa Mista Blinken, zai gana da shugaba Macky Sall, na Senegal, wanda ake sa ran zai zama shugaban kungiyar tarayyar Afrika nan gaba.

Gabanin Senegal, wacce ake wa kallon misali na gari na mulkin demokuradiyya a Afrika, sakataren harkokin wajen Amurkar, ya ziyarci kasashen Kenya da Najeriya.

A Kenya dai ya tattauna da mahukuntan kasar kan rikicin Habasha da matsalar tsaro a Somalia, sai kuma halin da ake ciki a Sudan.

A Najeriya kuwa Blinken, ya bayyana manufofin Amurka a Afrika.

342/