Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

20 Nuwamba 2021

14:51:11
1200474

​Hamas Ta Mayar Wa Burtaniya Da Martani Kan Saka Ta Cikin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa inda ta mayar da martani kan matakin da sakataren harkokin cikin gida na Burtaniya ya dauka na sanya kungiyar cikin 'yan ta'adda, bisa tuhumar Hamas da kokarin kawar da Isra’ila da kuma neman kafa gwamnatin musulunci a Falastinu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bayanin na Hamas ya ce; sakatariyar harkokin cikin gida ta Buritaniya, Britt Patel ta kira kungiyar Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci tare da yi wa magoya bayanta barazanar daurin shekaru 10 a gidan yari.

Sai dai abin takaicin shi ne, Buritaniya tana ci gaba ne da maimaita wautar da ta yi a baya, maimakon ta nemi gafarar al'ummar Palastinu da kuma gyara kuskuren tarihi da ta yi wa wannan al'umma, dangane da mummunan kudirin Balfour ya dauka, da kuma mulkin mallakar Burtaniya a kan Falastinu, wanda Burtaniya ce ta mika Falastinu ga yahudawan sahyuniya domin su mayar da ita kasarsu, inda tare da taimakon Burtaniya yahudawa suka kafa Isra'iila a cikin Falastinu.

Bayanin ya ce wannan ya ishi Burtaniya abin kunya a tarihi har kasa ta nade, amma kuma ba ta takaitu da hakan ba, har sai ta sake dawowa tana taimaka ma Isra'ila domin murkushe al'ummar Falastinu masu gwagwarmayar neman 'yancinsu da rayuwa cikin karama da mutunci.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, keta alfarmar wurare masu tsarki da kuma tsorata masu ibada da tozarta su, da kwace wurare na al'ummar Falastinu da gina matsugunnan yahudawa 'yan share wuri zauna da Isra'ila ke yi da kai hare-hare a kan fararen hula da yi musu kisan gila, wanann shi ne ta'addanci na hakika.

Ofishin jakadancin gwamnatin Falastinu da ke Landan ya yi kakkausar suka kan matakin na gwamnatin Burtaniya, tare da bayyana hakan a matsayin halasta abin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi da cin zarafin al’ummar Falastinu.

Kungiyoyin Falastinawa suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan mataki na gwamnatin Burtaniya, tare da jaddada goyon bayansu ga Hamas, da kuma dukkanin kungiyoyi masu gwagwarmaya domin kubutar da Falastinu daga mamayar yahudawan sahyoniya.

Yanzu haka dai sakatariyar harkokin wajen kasar ta Burtaniya tana shirin mika wannan daftrain kudiri ga majalisar dokokin kasar domin kada kuri’ar amincewa ko rashin amincewa da shi.

342/