Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

19 Nuwamba 2021

11:04:30
1199983

Shugaban Hukumar IAEA, Zai Kawo Wata Ziyara Tehran Ranar Litini

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Rafael Grossi, zai kawo wata ziyarar aiki a birnin Tehran ranar Litini.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ziyarar tasa dai na zuwa ne yayin da ake sa ran komawa bakin tattaunawar Vienna mai manufar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, a ranar 29 ga watan Satumba nan.

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Saeed Khatibzadeh, ta ce yayin ziyarar tasa shugaban hukumar ta IAEA, Rafael Grossi, zai gana da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian, da kuma shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami.

Tattaunawar ta Vienna dake tafe yayinta Iran na fatan za’a dage mata takunkuman da tsohuwar gwamnatin Amurka ta kakaba mata, haka ma komawar Amurka a cikin yarjejeniyar ta 2015 na daga cikin ajandar tattaunawar ta bakwai da akae sa ran komawa a karshen wannan wata.

342/