Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

14 Nuwamba 2021

11:36:32
1198394

​Amurka Ta Na Boye Kisan Kiyashin Da Ta Yi Wa Mata Da Yara 64 A Siriya

<h4 "="">Gwamnatin kasar Amurka tana kokarin boye wasu hare-haren da ta kai lardin Dayr Al-Zawr na kasar Siriya a shekara ta 2019 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula mata da yara 64.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta bayyana cewa harin da sunan yaki da kungiyar Daesh ya auku ne a ranar 18 ga watan Maris na shekara ta 2019 a garin Bagooz da ke gabacin lardin Dayr Alzawr inda mata da yara 64 suka rasa rayukansu.

Lawyoyin da suka fahinci al-amarin sun bayyana cewa wannan harin zai iya zama laifin kissan kare dangi wanda yakamata a hukunta duk wanda ya aikata hakan.

Amma gwamnatin Amurka ta yi rufa rufa da al-amarin, sannan ta yi ta bada hujjoji wadanda suka hada da cewa akwai wata mata da wani yaro guda rike da makamai a hotunan da aka nuna a lokacin kai harin.

A shekara ta 2014 sojojin Amurka da kawayenta suka shiga kasar Siriya da sunan yakar kungiyar yan ta’adda ta Daesh wacce ita kafa ta, sai dai don cimma wasu manufofinsu a kasashen Siriya da Iraki da kuma kasashen gabas ta tsakiya.

Sannan rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Amurka su na taimakawa mayakan na Daesh a wannan yakin, ta na daukarsu daga wuri zuwa wasu wurare don su kifar da gwamnatocin kasashen Iraki da Siriya a lokacin.

342/