Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Omar tana fadar haka a jiya Jumma’a ta kuma kara da cewa majalisar dokokin kasar Amurka tana da karfin hana wannan cinikin, kuma Amurka bai kamata ta saida makamai ga kasashen da suke take hakkin bi’adama ba.
Labarin ya kara da cewa wannan bukatar ta Omar ta zo ne a lokacinda Amurkawa da dama suke nuna damuwarsu da irin yadda gwamnatin kasar Saudia take kissan mutanen kasar Yemen.
A ranar 4 ga watan Nuwamban da muke ciki ne gwamnatin shugaba Biden ta bada sanarwan cewa ta sayarwa kasar Saudiya karin makamai masu linzami wadanda ake cillasu daga sama zuwa kasa har 280 a kan kudi dalar Amurla miliyon $650.
342/