Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Asabar

13 Nuwamba 2021

16:29:53
1198126

MDD: Ta Yi Kira Ga Dukkan Jam’iyyun Siyasa A Libiya Su Shiga Zaben Da Za’a Yi A Kasar

Babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres yayi kira ga dukkan jam’iyun siyasar kasar libiya da suka shiga a dama da su a dukkan zabubbukan da za’a yi a kasar, wadanda suka hada da na shugaban kasa da na yan majalisu a duk fadin kasar a karshen wannan shekara, da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ya kara da cewa gudanar da zabe shi ne mataki na gana da zai shimfida taswirar hanyar samar da zaman lafiya da tabbaci a kasar, kana yayi gargadin cewa duk wata jamiya da ta yi kokarin yin kafar ungulu na neman kawo cikas ga zaben da ake shirin yi za ta biya farashi mai tsada akan haka,

Za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisu ne a ranar 24 ga watan Decemba mai kamawa ,

A wani taron da aka gudanar a birnin Paris day a samu halartar shuwagabanin wasu kasashe har da kasar masar an bukaci a gudanar da zaben a lokacin da aka tsara.

342/