Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

6 Nuwamba 2021

13:18:28
1196042

Amurka Ta Sanya Kamfanin Pegasus Na Isra'ila A Cikin Jerin Haramtattu

Amurka ta sanar da sanya sunan kamfanin Pegasus na Isra’ila wanda aka bankado ana amfani da manhajarsa ta NSO wajen yin leken asiri, cikin jerin haramtatun kamfanoni a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ma’aikatar kasuwancin AMurka, ta ce an dau wannan matakin ne saboda dalilai na tsaro.

Kamfanin na Pegasus, shi ne mallakin manhajar nan ta leken asiri da aka yi wa fitatun mutane da manyan jami’an gwamnati da shugabannin kasashe ciki har da na faransa Emanule Macron kutse ta waya.

A sakamakon bincike da aka fitar watannin an nuna yadda akayi amfani da manhajar Isra’ilar, wajen yi wa ‘yan fafatukar kare hakkin dan adam da ‘yan jarida da kuma ‘yan hammaya a fadin duniya kuste.

Kamfanin na Isra’ila wanda aka kafa a 2011, ya jima yana fakewa da cewa, manhajarsa ana amfani da ita ne domin samun bayanai daga gungun masu aikata manyan laifuka ko ‘yan ta’adda.

Saidai kungiyoyi irinsu Forbidden Stories, da Amnesty International, sun ce daga shekarar 2016 sun fitar da lambobin waya na masu mu’amula da kamfanin na NSO 50,000 da aka zaba domin sanya ido akansu.

342/