Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

4 Nuwamba 2021

11:42:49
1195425

MDD Ta Aike Da Kayan Agaji na Kiwon Lafiya Zuwa Afghanistan

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta sanar da cewa an aike da kayan taimako na kiwon lafiya ton 229 zuwa kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Taimakon ya hada da magunguna wanda hukumar lafiya ta duniya ta ce zai wadatar da mutane miliyan 2.7 a kasar ta Afghanistan.

Haka nan kuma hukumar ta sanar da cewa za ta aike da karin kayayyakin kiwon lafiya a makonni masu zuwa.

Ana aike wa da kayayyakin jinyan ne zuwa kasar Afganistan bayan da hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin rugujewar tsarin kiwon lafiya a kasar, tare da yin kira ga kasashen duniya da su taimaka cikin gaggawa.

342/