Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

5 Oktoba 2021

14:29:02
1186050

Shafukan Sadarwa Na Facebook da WattsAppa sun dawo suna aiki amma rabi da rabi

Shafukan sadarwan na facebook da wattsAppa da kuma Instgram wadanda suka bar aiki kwata-kwata na 'yan sa'o'ii a jiya sun dawo aiki amma ba kamar yadda suke a da ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Masu amfani da wadannan shafuka a duk fadin duniya sun bayyana cewa sun dawo amma har yanzun basu koma kan yadda suke a da ba.

Kafin haka dai bangaren inginiyoni na kamfanin facebook sun bayyana kan shafin kan cewa sun dawo aiki sa'o'i bayan da suka dakata. Har'ila yau Jaridar NewYork Times ta bayyana cewa kamfanin facebook ya aike da ma'aikatansa masana zuwa cibiyar kayakin aikinsa da ke jihar calfoniya inda suka gabatar da ayyuan gyara gaba da gaba ba ta na'urorinsadarwa ba.

Kimar wadannan kamfanonin sadarwa dai sun fadi a kasuwannin jari a duniya bayan dakewa na wasu sa'o'i.

342/