Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

2 Oktoba 2021

14:31:45
1185092

​Iran: Takunkuman Tattalin Arziki Sun Hana Kasar Samun Magungunan Corona Da Sauri

Gwamnatin kasar Iran ta zargi Amurka da hanata samun magungunan cutar corona a cikin lokacin da ya dace. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Qurbanpoor daya daga cikin jami’an diblomasiyyar kasar a MDD yana fadar haka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ya kuma bayyana haka ne a wani jawabin da ya gabatar a gaban kwamiti na ukku kamar yadda suke kiransa a MDD, ko kuma wanda ake kira ‘the Social, Humanitarian and Cultural Committee or SOCHUM ko C3)’.Qurban poor ya kara da cewa abinda wasu ke cewa an dage takunkuman tattalin arziki kan magunguna wa kasar ta Iran karyace a fili.

Dangane da kasar Falasdinu da aka mamayte kuma, Qurbanpoor ya ce haramtacciyar kasar Isra’ila ta na aikata laifuffukan yaki da neman shafe wata al-umma daga doron kasa, amma abin mamaki shi ne yadda kasashen duniya suka yi gum da bakunansu, har sai da abin ya zama jiki ko kuma aka manta da shi.

342/