Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

28 Satumba 2021

07:56:29
1183731

Mikdad : Dole Amurka Da Turkiyya Sun Janye Daga Arewacin Siriya

Ministan harkokin wajen Siriya Faisal Mekdad ya caccaki Amurka da Turkiyya saboda mamaye yankunan da ke cikin kasar, inda ya yi kira ga Washington da Ankara da su janye sojojinsu ba tare da wata wata bas u kuma su daina “wawashe” dukiyar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A cikin jawabinsa ga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin, Mikdad ya ce yakin da Siriya ke yi da ta'addanci zai ci gaba har sai an kawar da dukkan yankunan Siriya daga barazanar.

Mikdad, ya ce gwamnatin Damascus tana aiki don kawo karshen mamayar kasashen waje na yankunanta ta kowace hanya da doka ta tanada.

Ministan harkokin wajen na Siriya ya kuma yi Allah wadai da takunkumin karya tattalin arziki da aka sanya wa kasarsa da wasu kasashen duniya irinsu Cuba, Iran, Venezuela da Yemen, inda ya bayyana takunkumin da toye hakkin dan adam, da haddasa mace mace, da wargaza sha’anin kiwon lafiya, da hadassa matsalolin abinci da rayuwa.

Siriya tana cikin kasashen da hare-haren ta'addanci suka fi shafa wandan ‘yan ta’adda suka mamaye wasu jihohin kasar, hakan ya sa ayyukan ta’addanci suka haifar da kisan wadanda basu ji basu gani ba, rashin tsaro, lalata muhimman ababen more rayuwa, sace dukiyar kasa da haifar da rikicin a cikin kasar.

Amma a cewar Mikdad, ‘’bisa jarumtakar mutanenmu da sojojinmu, da taimakon abokanmu, mun sami nasarori na musamman a yakin da muke yi don kawar da ta'addanci,"

Ya ci gaba da cewa gwamnatin Turkiyya na ci gaba da tallafawa ayyukan ta'addanci a Idlib, inda ta mai da lardin arewa maso yammacin Siriya mafaka ga 'yan ta'adda na kasashen waje.

342/