Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

26 Satumba 2021

14:13:06
1183328

Mazhabar Katolika Ta Nemi Afwa Kan Kisan Kiyashin Da Aka Yi Wa ‘Yan Asalin Kasar Canada

Coci-Cocin mazhabar Katolika ta kiristoci sun nemi amfawa bisa abinda jami’an cocin suka aikata na kisan kiyashin yara ‘yan asalin kasar Canada a makarantun kwana wadanda suke karkashin kulansu kimani shekaru 100 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : na kasar Iran ya nakalto majiyoyin coci-cocin na katolikan ta na fadar haka bayan gano kaburburan gama gari har guda 3 na yara ‘yan asalin kasar Canada wadanda aka gano a wasu jihohin kasar ta Canada a cikin wannan shekarar, wanda yawansu ya kai 1,200 ya zuwa yanzu. Kuma har yanzun ana ci gaba da amfani da wasu na’urorin Rada don gano karin irin wadannan kaburbura.

Bayan mamayar da turawan suka yiwa kasar Canada a karnuka da suka gabat malaman mazahbar katolika sun bude makarantu na kwana, inda suke kula da ‘ya’yan kabilun da suka samu a kasar, amma kuma a boye suka kashe da dama daga cikinsu.

Shuwagabannin kabilun asalin kasar Canada sun ce za su amince da wannan afwa, amma suna son wata dawaga daga kasar ta je kasar Italiya don ganawa da paparoma kan batun kafin ya kawo ziyarar ganin ido kasar.

342/