Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya nakalto Badr Zayidi mamba a kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar ta Iraki yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa ficewar sojojin Amurka daga kasar Iraki yana zuwa ne bisa yarjejeniyar da Amurkan da cimma da gwamnatin Mustafa Al-kazimi a ckin watan Yunin da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu akwai sojojin Amurka kimani 2500 a cikin kasar Iraki, sannan zuwa ranar daya ga watan Jenerun shekara ta 2022 ba wani sojoan Amurka da zai rage a kasar, sai wadanda zasu ci gaba da horas da sojojin kasar da kuma bada shawara.
342/