Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

14 Satumba 2021

09:56:27
1179698

MDD, Ta Samu $ Biliyan Guda Domin Tallafawa Afghanistan

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ta samu sama da Dala Biliyan guda na tallafi domin agazawa al’ummar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tallafin ya samu ne bayan taron kasa da kasa da aka gudanar ranar Litini a Geneva domin samar wa da kasar ta Afghanistan tallafi.

Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya yi fatan tallafin zai taimaka wajen ayyukan kare hakkin dan adam a wannan kasa ta Afghanistan.

Kimanin ‘yan Afghanistan miliyan 11 ne ke bukatar tallafin jin kai a cewar MDD.

Mista Guteress, ya bukaci da a tattauna da kungiyar Taliban dake mulki a kasar, saboda a cewarsa ba yadda za’a shayo kan halin da ake ciki a kasar ba tare da damawa da ‘yan Taliban ba.

‘’Ya kuma babu wata riga ga kakaba wa kungiyar Taliban takunkumi’’.

342/