Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Asabar

11 Satumba 2021

13:02:51
1178977

An Kai Harin Roka Kan Sansanin Amurka Da Ke Garin Al-Shadadi

An harba makamai masu linzami guda biyu kan sansanin sojojin Amurka da ke garin Al-Shadadi da ke wajen kudancin Al-Hasakah.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -Abna, rokoki biyu sun fadi a sansanin sojin Amurka da ke garin Al-Shadadi a kudancin unguwar Al-Hasakah a yau. Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam ta Syria (mai alaka da 'yan adawa) ta ba da rahoton cewa wasu masu fafutuka sun ba da rahoton rokoki biyu. Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin dan adam ta Syria ta cewa watakila harin na da alaka da kungiyar ta'adda ta ISIS na da hannun ta aciki na kokarin kai hari wannan sansanin.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu asarar rayuka ba, kuma bayan harin sojojin sun shiga cikin shirin ko -ta -kwana tare da yin bincike a yankin.

342/