Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

2 Satumba 2021

12:53:58
1175901

‘Yan Adawa A Venezuela Zasu Shiga Zabe, Bayan Shekara 3 Na Kauracewa

Manyan jam’iyyun adawa a Venezuela, sun bayyana cewa zasu shiga a dama dasu a zabukan kananan hukumomi dana jihohi da za’a yi a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Wannan dai shi ne karo na farko, bayan da jam’iyyun adawan ke kauracewa zaben a cikin shekaru uku.

Matakin dai ya kawo karshen kaucewar da ‘yan adawan kasar ke wa zaben, wanda suke dangantawa da marar tabbas akan sahihancinsa.

Jam’iyyun adawan dai na tunanin kafa kawance mai karfi, irin wanda ya basu damar yin nasara a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na 2015.

Shigar ‘yan adawan kasar a zaben na zuwa ne bayan soma wata tattaunawa a watan Agusta a Mexico, tsakanin wakilan gwamnati da na ‘yan adawan kasar.

342/