Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

2 Satumba 2021

12:50:35
1175898

Siriya: Rokoki Sun Fada Kan Cibiyar Kawancen Amurka Masu Yaki Da Daesh A Arewacin Kasar

Majiyar tashar talabijin ta Almayadeen tv daga kasar Siriya ta bada sanarwan cewa an cilla makaman roka kan cibiyar yaki da kungiyar Daesh ta kasa da kasa da ke wajen birnin Dair-Zur na arewacin kasar ta Siriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Labarin ya kara da cewa an cilla makaman rokan ne da misalin karfe 8 na yammacin jiya Talata, kuma harin ya haddasa asarorin dukiya masu yawa amma babu labarin ko akwai asarar rayuka.

Majiyar ta kara da cewa mayakan kungiyoyin ‘yan ta’adda masu samun mafaka a cibiyar sun rikice.Banda haka wata majiya ta bayyana cewa makaman sun taso ne daga yankunan da sojojin Siriya suke iko da su a yankin, jiragen yakin kawancen sun yi ta shawagi daga bayan a kan yankin har zuwa tsakiyar dare, amma babu labarin kai farmaki ko luguden wuta a wani wuri a yankin.

Cibiyar kawancen Amurka da sunan yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh dai ba bisa ka’ida aka kafa ta ba, don bata sami izinin gwamnatin kasar Siriya ba.

342/