Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Abna 24
Alhamis

2 Satumba 2021

12:39:02
1175895

Hamas: Ficewar Amurka Daga Afghanistan Lokaci Ne Da Ya Shiga Tarihi

Shugaban ofishin siyasa na Hamas ya ce: "Ficewar Amurka daga Afganistan wani juyi ne na ci gaban yankin kuma yana dauke da sakon cewa nufin yunkurin al'ummomi ya fi karfin Yan mamaya.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA ya ruwaito, "Sami Abu Zuhri", daya daga cikin jami'ai kuma shugaban sashin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Falasdinu (Hamas) a kasashen waje, ya rubuta a shafinsa na Twitter: Kammala Janye sojojin Amurka daga Afganistan wani lokaci ne na tarihi, Babbar nasara ce ga mutanen Afghanistan da Taliban.

Ya kara da cewa: "Wannan abun da ya faru wani juyi ne a fagen ci gaba a yankin kuma yana isar da sako ga duk abin da al'ummomi suek buri da yinkuri yi fi karfi fiye da na yan mamaya.

342/